2 Maris 2019 - 17:35
Iran Ta Bukaci Samar Da Sulhu Tsakanin Hidia Da Pakistan

Sakamakon rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen Pakistan da India, kasar Iran na kokarin ganin an yi sulhu a tsakanin kasashen biyu.

Tashar presstv ta bayar da rahoton cewa, Ministan harkokin wajen Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif yana ci gaba da tuntubar gwamnatocin kasashen India da Pakistan, a yunkurin da kasar Iran take yi na shiga tsakanin kasashen biyu domin sulhunta su.

Rahoton ya ci gaba da cewa, kasar Iran tana ganin rikicin India da Pakistan lamari ne mai matukar tayar da hankali, domin dukkanin kasashen biyu suna da tasiri sosai a yankin, kuma duk wani takun saka a tsakaninsu zai cutar da yankin ne baki daya.

A kan haka Iran ta sha alwashin ganin cewa ta yi iyakacin kokarinta, domin ganin an samu sulhu da fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu, inda yanzu haka ministan harkokin wajen kasar ta Iran yake ci gaba da tuntubar bangarorin biyu kan hakan.

Dukkanin kasashen biyu, wato India da Pakistan suna da kyakkyawar alaka da kasar ta Iran.